ads:::

APC da Buhari 'sun jefa 'yan Najeriya cikin matsananciyar yunwa

APC da Buhari 'sun jefa 'yan Najeriya cikin matsananciyar yunwa'

Atiku ya ce APC ta zama jam'iyyar mayaudaraHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionAtiku ya ce APC ta zama jam'iyyar mayaudara
Dan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa jam'iyyar APC mai mulki da shugaban kasar Muhammadu Buhari sun jefa 'yan Najeriya cikin matsananciyar yunwa.
Sai dai APC ba ta yi raddi kan wannan zargi ba.
Sanarwar da kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya fitar ta ambato dan takarar na PDP yana bayyana haka a birnin Gombe inda ya je yakin neman zabe ranar Talata.
Da yake jawabi ga magoya bayansa, tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya ce a fiye da shekara uku da rabin da APC ta yi a kan mulki "ta shirga wa 'yan kasar karya" wajen yin alkawuran kawo sauyi.
"A shekarar 2015, jam'iyyar APC ta yi alkawuran samar da abinci, amma yau muna cikin yunwa. PDP ta dawo domin ceto mutane daga radadin talauci da wahalar da APC ta jefa su a ciki", in ji Atiku Abubakar.
APC dai ba ta ce uffan kan wannan zargi ba, ko da yake ta sha cewa PDP da dan takarar ta ba su da manufofin ciyar da Najeriya gaba shi ya sa ko da yaushe suke yin irin wadannan zarge-zarge.
Masana harkokin siyasa na ganin jam'iyyun biyu za su ci gaba da kushe juna a yunkurin da suke yi na ganin sun gamsar da masu zabe a 2019.
Wannan layi ne
atiku abubakarHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Tarihin Atiku Abubakar a takaice
  • Shekararsa 72
  • Ya zama gwamnan jihar Adamawa
  • Ya yi mataimakin shugaban kasa 1999 zuwa 2007
  • Hamshakin dan kasuwa ne
  • Ya rike mukami a hukumar Customs
  • Ya sha fuskantar zarge-zargen cinhanci da rashawa
  • Musulmi ne daga arewacin Najeriya

Post a Comment

0 Comments

Contact Form

Name

Email *

Message *

Translate

LATEST POST