ads:::

Yan sa-kai na 'kashe mutane a kasuwannin Zamfara'

Yan sa-kai na 'kashe mutane a kasuwannin Zamfara'


Matsalar tsaro ta salwantar da rayukan mutane da dama a ZamfaraHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMatsalar tsaro ta salwantar da rayukan mutane da dama a Zamfara

Wasu al'ummomi a jihar Zamfara ta Najeriya sun kaurace wa kasuwannin kauye saboda yadda wasu da ake kira 'yan sa-kai ke shiga suna kashe mutane da sunan farautar barayi da 'yan fashi.
Kasuwar Jangebe a karamar hukumar Talatar Mafara na daya ga cikin babbar kasuwar kauye da ke ci duk Lahadi a zamfarar.
Fulani da mutanen kauyen da ke cin kasuwar sun ce 'yan sa-kai na shiga kasuwar su kama sannan su kashe mutanen da suke zargi suna da alaka da barayi.
A cewar 'yan kasuwar wannan al'amari ya dagula kasuwancinsu da kuma jefe fargaba a zukatan mutane.
To sai rundunar 'yan sanda jihar ta ce ba ta da masaniya a kan wannan al'amari.
A tattaunawarsa da BBC, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandar jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ce jami'ansu na taka muhimmiyar rawa wajen kawar da bata gari da kokarin inganta tsaro a kewayen kauyuka da birnin Jihar.
Sai dai ya ce la'akari da matsalolin tsaro da jihar ke fama da su kowa na da alhakin tuntubarsu ko bada gudunmawa wajen kawar da masu tada kayar baya.
SP Muhammad ya kuma umarci kowanne mutum ya kasance mai sa ido da ankarar da jami'an tsaro a duk lokacin da aka fuskanci wasu na kokarin tada zaune tsaye.
Hare-haren da barayin shanu da masu satar mutane don kudin fansa ke yi a Zamfara na karuwa a baya-bayan nan, duk da yunkurin jami'an tsaro na kawo karshen ayyukansu.
Gwamnatin jihar ta sha cewa tana daukar mataki domin shawo kan matsalar, ko da yake ana zarginta da hannu a batun amma ta musanta zargin.

Wannan layi ne

Karin bayani game da Zamfara:

  • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
  • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
  • Take: Noma tushen arzikinmu
  • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
  • Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
  • Musulmi ne mafi yawa
  • Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000
  • Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu

Sharhi kan tarihin rikice-rikice a Zamfara - Daga Kadariyya Ahmed

Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar Zamfara.
A yayin da matsalar barayin shanu ta zama bala'i ga jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari ya samar da kungiyar 'yan kato da gora don yakar maharan a shekarar 2013.
Sai dai ba a dauki dogon lokaci ba mazauna yankin suka fara korafi kan 'yan kato da gorar, wadanda a yanzu su ma suke gallabar mutanen da ya kamata su kare da sace-sace.

Ana zargin cewa yaran Buharin Daji (mai rike da lasifika) ne, wanda aka kashe farkon watan Maris ke ci gaba da aikata fashi
Image captionAna zargin cewa yaran Buharin Daji (mai rike da lasifika) ne, wanda aka kashe farkon watan Maris ke ci gaba da aikata fashi

Hakan ta sa kauyukan da ke fama da matsalar barayin shanu da 'yan kato da gora suka fara kokarin ganin sunkare kansu da duk abun da ya kamata.
Daga haka sai rikicin ya kara ruruwa ta hanyar kai hare-hare da daukar fansa. A haka sai a ka kasa cimma kokarin shirin yin afuwa da aka so gabatarwa.
A yanzu dai muna ganin yadda rikici ke kara bazuwa da karuwa kuma ga alama ba a san hanyoyin da za a bi a shawo kansa ba.
Abun da yake a bayyane kawai shi ne yadda dumbin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ke ci gaba da mutuwa.

Post a Comment

0 Comments

Contact Form

Name

Email *

Message *

Translate

LATEST POST