ads:::

SOYAYYA CE

SOYAYYA ita ce tushen rayuwa mai inganci da ke kawo zaman lafiya a cikin rayuwar mu ta yau da kullum, ka s

Wannan tambaya an dad’e ana kaiwa da kawowa a kanta, masana da yawa sun tattauna domin ganin sun samar da ma’anarta domin a gane ta a kuma fahimce ta. Kamar haka:

Soyayya ita ce nuna ‘kauna daga 6angarori biyu na masu ‘kaunar juna (https://arewapress1.blogspot.com/).

Muhammad Hashimu ya bayyana cewa: ‘Soyayya ita ce ni’ima mafi d’aukaka da Allah Ya ba wa bayinsa. Soyayya ita ce zuciyoyi biyu a dun’kule su cure, su game cikin zuciya d’aya. Haka kuma soyayya ita ce rai biyu cikin jiki d’aya. Soyayya ita ce mutum biyu cikin mutum d’aya. Abin da ake nufi a nan shi ne, idan mutum ya so wani tsananin soyayya sai ya zama cewa koda yaushe cikin tunaninsa yake, ba ya damuwa da kowa sai shi, ba ya son ji da ganin kowa sai shi, wato kenan sun zama mutum d’aya cikin jiki biyu.’

Duk da abubuwan da muka ambata hakan ba zai sanya mu ce mun bayyana ha’ki’kanin ma’anar soyayya ba. Domin ita soyayya ba za a iya siffanta yadda take ba. Sai mutum ya shige ta, sannan zai san ta.

KASHE-KASHEN SOYAYYA.

Soyayya ta kasu izuwa gida uku kamar haka:

1 Soyayya Don Sha’awa.
2 Soyayya Don Abin Duniya.
3 Soyayya Ta Ha’ki’ka Ko Gaskiya.

1-SOYAYYA DON SHA’AWA: A wani lokaci mace kan ga namiji ko kuma namiji ya ga mace, sai d’aya daga cikinsu ya ga wani abu a jikin d’ayan har ya ja hankalinsa ya ba shi sha’awa, ya ji yana son wannan mutum saboda wannan abu. To irin wannan ba soyayya bace sha’awa ce da zarar d’aya daga ciki ya biya bu’katar tashi sai a fara neman hanyar rabuwa da juna.

2-SOYAYYA DON ABUN DUNIYA: Irin wannan soyayya Ita ce wadda ake yi don kud’i, ko dan kyau ko dan wani ‘kyale-‘kyalen duniya. Ita ma irin wannan soyayya ba ta cika nisa ba, da zarar abun da ake yin soyayyar dan shi ya gushe, sai a fara shirye-shiryen nesanta da juna.

3-SOYAYYA TA HAK’IK’A KO GASKIYA: Irin wannan soyayya ita ce wadda ake amfani da hankali da tinani wajen kafa ta. Duk soyayyar da ba a gina ta a kan sha’awa ko wani abun duniya, ko wani mugun nufi ba, to wannan soyayya ta gaskiya ce. Kuma ita ce irin soyayyar da take d’orewa wadda ba ta yankewa har abada.

MENENE SO DA KAUNA.
 
So da kauna, wani shauki/hali ne wanda ke kama da juna wurin tantancesa a ilimance, haka kuma a aikace .
 Ka santuwar cewa ba kowa ke sanin abunda yake aikatawa ba a tsakanin mu, ko kuma, me masoyina masoyiyata ke yi man daga cikin wannan halaye. Kowannen anayinsu ne ba tare da mutum yasan me yake aikatawa ba, kasancewar baya iya tantancewa tsakanin biyun nan me suke nufi. Ko wannen su aikatasu halal ne a addinin muslumci, saidai wani yafi wani, daraja a idan shari'a kasancewar muhimmancin sa da amfaninsa tsakanin masoya. Hmm nasan wasu zasuyi mamaki akan cewar me ya hada addini da soyayya, tirqashi... To ka sani Madarar da zumur ilimin soyayya tatacce daga addinin muslunci, yake. Haka kuma duk wanda yabi tsarin soyayya a muslumci, ba shakka zai yi soyayya wacce take tatatta, kuma amintatta. Wacce babu yaurada ko ha'incin juna tsakanin masoya. 
 
Menene Kauna?
= Kauna tamkar SO take sai daifa tafi So aminci, domin ita kauna bata canzawa, kuma ita kauna ba’a amutu akanta, ma’ana ba’acewa lallai sai an auri wanda ake Kauna ko sai an kasance tare dashi, in hakan bata yuwuba za’ai tashin hankali, ko a fara zargin shi abin kaunar, ita kauna ba haka takeba, ko anyi nasarar samun abin kaunar ko ba’ayiba, ana cigaba da masa fatan alheri kamar yadda kake masa a baya. Kuma ita kauna bata kwaranyewa, rashin haduwa tsawan zamani bai kwaranyar da ita.
Galibi abinda ke kawo kauna dabi’une, wato halaiyan abin kaunar suke janyo zuciya zuwa ga kaunarshi.
 
 
1. SO ne sinadarin dake sanyaya zuciya kamar yadda freezer ke sanyaya zazzafan ruwa zuwa kankara.
2. SO ne tsuntsun dake kaikawo tsakanin zukata mabanbanta daga karshe har sai ya sami zuciyar da zai gina shekarsa.
3. SO ne dausayin farin ciki mai haddasa ruruwar farin ciki mara misali.
4. SO ne siffar samin ingantacciyar rayuwa mai alfanu.
5. SO ne tsaunin rahama mai sanya masoya magagi gami da shantakewa a bisa tagwayen manufofi.
6. SO ne fitilar dake haskaka zuci yayinda ta fada cikin duhu matsananci.
7. SO ne tekun dake gudana tsakanin zukata mabanbanta.
8. SO ne asalin rayuwa, sannan kuma abin dake sarrafa ragamar dokin rayuwa a bisa hanya managarciya.
9. SO ne mafarar kauna, sai so ya sami kyakkyawan mazauni a zuci kafin kauna ta biyo bayansa.
10. SO ne bishiyar dake tsirowa a dausayin zuci, mai fitar da furanni kyawawa masu kyawun gani.
11. SO ne sadaukin zuci, mai ingiza zuciya filin dagar kauna, har sai ya kafa tutarsa a bainar zuciya.
12. SO ne ginshiki, sannan kuma tubalin kauna sai an kafa tubalin so a zuci kafin ginin kauna ya tabbata a matabbatar ruhi.
13. SO ne tekun dake gangarowa daga ruhi zuwa sassa daban-daban na jiki, wanda ke fesar da shauki a nahiyar kalbi.
14. SO ne maganin dake warkar da zuciyar data shiga garari.
15. SO ne guguwar dake daukar, masoya, idan guguwar so ta dauki masoya takan makantar da idanuwansu har su rasa ganin laifin juna.
 
 

*Banbanci tsakanin SO da KAUNA

Shi so sau da dama idan masoyi bai samu nasarar samun abin san nashiba, sai ka ga wannan soyayyar ta koma kiyayya, wasuma har kaga sunawa abin san nasu fatan shiga uku, Allah ya rabamu da irin wannan SO

Ita kauna bata canzawa


* Abubuwan da ke janyosu (SO+KAUNA)
Duk abu dayane sai dai daga lokacin da aka ji zuciya tana raya cewa, in ba’a samu wanda a ke so ba, gara a mutu kowa ya rasa, hakan seya nuna mana ciwa So ake yi ba Kaunaban. A takaice dai SO tsakani da Allah shi ake kira Kauna.

Abubuwan dake janyo SO + Kauna

– Kyau
– Kudi
– Nasaba (Dangi)
– Addini
– Ilimi
– Gaskiya
– Amana
– Kunya
– Kyauta. DS

 

Kalaman Baki (SO)

* Da Idanuna basu gankiba> da bazan sankiba
* Da banga murmushi a kyakykyawar fuskarkiba> da ba zan So ki ba
* Da kunnuwana basu ji sautinkiba> da bazan jiki a zuciyataba

* Lafazinki dadi zuciya ta yake tausasa mini
* Kayan jikinki kamshi turaranki zo ki fesa mini
* Duniyata dake nake alfahari, Sarauniyar mata nasamu mai kwantarmin da zuciyata, Na baki kaina kirike……

YADDA ZA KA BAYYANAR DA SOYAYYARKA.

“Wata yarinya na gani na kuma kamu da sonta, kuma ina zuwa gidansu, yaya zan yi na bayyana mata ina son ta?”

AMSA.

Zata iya kasancewa babba ce ko ‘karama, to koma dai yaya take a karon farko akwai bu’katar kafin ka furta mata da baki, kake nuna mata wasu alamomi da zasu ke bayyana mata hakan a zahiri. ta hanyar fifita ta fiye da sauran ‘yan gidansu.

Idan ka tashi zuwa gidan da wata tsaraba ko wata kyauta ya kasance tata ta fi ta kowa yawa. Idan salla ta zo ka d’inka mata kayan salla da takalmi da sauran kayan kwalliya na mata dai-dai ‘karfinka ka aika ko ka kai mata su. A lokacin azumi kake aika mata da kayan shan ruwa.

Idan ka je gidansu ko da bata nan kake tambayar ina ta tafi, idan kuka had’u ka sanar da ita ka je gidansu dan ka gan ta ku gaisa amma sai aka samu akasi baku had’u ba, kuma baka ji dad’in rashin ganin nata ba.

Kake yawan jan ta da hira, kake bata labarai masu sanya nishad’i da d’ebe kewa a dukkan lokacin da kuke tare.

Na tabbata ko baka furta kalmar so a gare ta ba za ta sha’ku da kai, za ka ke burge ta, za ta ke son ganin zuwanka, haka kuma ‘yan gidansu za su fahimci ‘kudurinka na kana sonta.

Bayan an shafe tsawan wani d’an lokaci hakan na faruwa, sai ka ware watarana ka ziyarce ta har gida ka aika a kirawo ta ka sanar da ita batun da tuntuni take tsammanin ji daga wajenka, wato na kana son ta.

Zaka iya sanar da ita ta hanyar tura mata da sa’ko ko akasin haka, amma zuwa da kai, ya fi sa’ko.

Idan kuma yarinya ce zaka sanar da ita hakan ne bayan ta kai munzalin tsayawa da samari. Dama tintini ‘yan gidansu sun dad’e da sanin manufarka a kanta, har ta kai suna zolayarta da kai, wata’kila ma suna yi maka magana akan hakan ko kuma sun zuba ido suna jiran ka furta hakan da kanka.

Daga nan kuma sai a shiga mataki na biyu wato fagen soyayya.

YAUDARA A SOYAYYA.

Abun dai ruwan dare ne, ba ga mazan ko matan ba.

Kowane 6angare na maza da mata suna ta6a waccan halayya ta yaudara a soyayya kuma suna fuskantar hakan daga abokan zamansu.

To amma shin wai mene ne yake kawo yaudara a soyayya? Mece ce ma ma’anar kalmar yaudara?

Yaudara ita ce, hali na 6oye gaskiya da niyyar cuta ko zambatar wani.

A lokuta da yawa maza su ke sakin jiki har mata su yaudare su, ko kuma su mata suke sakankancewa har maza su yaudare su a soyayya. Ina ganin za ku yarda da ni idan na ce.

A dukkan lokacin da ka ji yaudara to da akwai rashin so da tausayi.

MAZA:

A sau da yawan lokuta namiji kan makance a kan soyayya har idanuwansa su rufe a kan haka, ya gaza gane macen da ta ke son shi dan abun hannunsa, ko ta ke kula shi kawai saboda rage dare, ko dan wani abu da ta ke nema a wajensa, ko macen da ta ke kula shi ba dan tana son shi ba, sai dan kawai ya matsanta mata akan ta so shi, da macen da ta ke son shi kawai dan tana jin dad’in kalamansa ko jin dad’in hira da shi amma ba dan tana son shi ba, har ta kai daga baya da zarar ta samu wani da take so ko ta gama cimma burinta a gare shi sai ta guje shi. Sai ka ji daga bisani ana mayar da yawu kan cewa ai wance ta yaudare ni, bayan kuma da ma can babu son gaskiya a tsakani.

Domin gujewa fad’awa irin wannan halin, tun da fari akwai bu’katar ka san wasu alamomi da ganinsu zai tabbatar maka da cewa tabbas wance tana sonka da gaskiya. Amma duk da haka sai ka yi taka-tsantsan.

MATA:

Ke ma akwai bu’katar dukkan wanda ya zo miki da batun soyayya, ki tsaya ki nutsu ki tantance masoyinki na gaskiya, domin gujewa fad’awa tarkon samarin shaho (‘yan-yaudara)

Akwai wani zai zo ne yana son ki kawai dan ya yi alfahari da cewa ke budurwarsa ce. Wani kuma zai yi ‘ko’karin neman hanyar da zai bi ya yaudare ki ne dan ya lalata miki rayuwa. Wani zai zo wajenki dan ya rage dare ne kawai. D.s.

Da yawan ‘yan yaudara, za su iya kashe miki ko nawa ne, har ma su yi wa waninki hidima, dan bu’katarsu ta biya a kanki. Sun iya kalamai masu dad’i amma na yaudara.

Maza ‘yan yaudara suna da wahalar ganewa a wajen mata, wani zai iya zubar miki da hawaye, wai dan duk ki yarda ya na son ki da gaskiya, zai iya siyo miki duk abun da kike so, zai iya baki duk abun da kika bu’kata daga wajensa matu’katar bu’katarsa za ta biya a kanki.

Domin gujewa hakan ya kamata kike lura da irin kalaman da yawanci ke futa daga bakinsu, kike tace na gaskiya da kuma na ‘karya. Karda SO ya rufe miki ido ki gaza tabbatarwa da zuciyarki wane yaudararki kawai yake son yi, bayan kin gano hakan ko alamun hakan sun bayyana ‘karara a zahiri, saboda gudun yin da-na-sani daga baya. Wanka da gari dai ba ya maganin yunwa.

 

Ma’anar Aure 
Abinda aka sani da aure a dukkan al’adu, yaruka da addinai shine namiji ya samu macen da yake, ya jawo hankalinta akan ta yarda suyi zaman tare, ya biya haqqoqinta sannan mutane su shaida akan cewa ta zama matarsa saboda haka an halatta masa yin duk wasu abubuwa da kan iya gudana tsakanin mace da namiji. Yana daga cikin al’adun kuma cewa daga ranar ita macen zata bar gidansu ta koma gidan shi wanda ta zaba kuma ta aura a matsayin mijin nata.
Akan daura aure tare sharudda da yawa wandanda suka banbanta daga al’ada zuwa al’ada. A al’ada da addini na bahaushe, sharuddan da sukan biyo aure sun hada da samarda muhalli ko gurin zama ga matar, ciyar da ita, sama mata tufafi da kuma kula da lafiyarta.


Dalilin Yin Aure


Akwai dalilai da yawa da suka sa dole duk wani mutum mai hankali yayi aure idan yakai munzalin yin auren. Annabin tsira (S.A.W) yace da al’ummarsa kuyi aure ku hayayyafa dan inyi alfahari da yawanku ranar qiyama. Sannan Allah SWT ya halicci mutane (maza da mata) da sha’awa, wacce hanya daya da duk addinai suka yarda da ayi amfani da ita wajen biyan buqatar sha’awa shine aure. Wadannan dalilai guda biyu ma kawai sun isa hujja ga masu cewa su basa soyayya; sai da soyayya ne za’a iya yin aure.
Idan aka duba bangaren ibada kuma, Annabi (S.A.W) yace wanda yai aure ya bayar da rabin ibadarsa, sannan duk wani abu da masu aure zasu yiwa junansu na daga jin dadi lada zasu samu, hmn wannan itace garabasa, hanya mai sauqi ta samun aljanna.
Yana da amfani mutum yasan wadannan manufofi na yin aure kafin yayi aure, sannan kuma ya dinga tuna su koda yaushe, musamman a lokacin da aka samu sabani, hakan zai taimaka wajen shawo kan da yawa daga cikin matsalolin aure. Haka shima wanda yaje yin sulhu ga ma’auratan da suka sami sabani, yana da kyau ya tunantar dasu akan wadannan manufofi na yin aure; Allah yasa mu dace.

 

WACCECE MACE TA-GARI??

1. Mace tagari ita ce wacce Idan Mijinta ya kalleta Zai ji farinciki ya lullubeshi.
2. Ita ce wacce take gaggawa wajen cika umurnin Mijinta.
3. Ita ce wacce take mutukar kiyaye duk abinda zai 'bata ma Mijinta rai.
4. Ita ce wacce take dagewa wajen bautar Ubangijinta.
5. Ita ce wacce batta wasa da duk wani Hakki na mijinta.
6. Ita ce wacce duk lokacin da Mijinta yayi fushi, batta samun kwanciyar hankali har sai ta yardar dashi.
7. Ita ce wacce take Kiyaye Duk wani sirrin Mijinta.
8. Ita ce wacce idan Mijinta ba yanan take Kiyaye mutuncin Kanta, da kuma dukiyar da ya bari agida.
9. Ita ce Wacce take kulawa da Tarbiyyan Mijinta da 'ya'yansa koda ba ita ce ta haifesu ba..
10. Ita ce wacce take mutukar girmama Iyayen Mijinta kamar yadda take girmama nata iyayen.. Kuma take kyautatawa 'yan uwansa ba tare da tsangwama ba.
11. Ita ce wacce take zama da Makobtanta da kishiyoyinta cikin tsoron Allah da kyautatawa. Koda su suna munana mata..

 

MIJI NAGARI ... KO KUNSAN WAYE MIJI NAGARI 


Most of the time a wajen wa'azozi ko lectures ba a cika fadawa mutane halayen miji nagariba abin yana yawan bani mamaki akan meyasa baacewa ga halayen miji nagari, sai dai ayita cewa halayen mace tagari.... Ga wassu daga cikin halayen miji nagari Shine wanda yake ciyar da iyalinsa halaliya idan shima yaci... Yake shayar dasu idan shima yasha.... Kuma yake tufatar dasu idan ya suturta kansa bawai sai shekara shekaraba domin yasan darajar kwalliyar.... Shine wanda zai zamo zaki a waje, damo acikin gida wato me hàkuri ga dukkan lumura... Ko kuma yazamto kamar air condition wato a waje yake kara amman aciki sanyi yake bayarwa.... Shine wanda ya hada wassu siffofi guda 10 wadanda Allah Ta'ala Ya ambacesu acikin suratul Ahzab aya ta 35. Miji nagari shine wanda yakeson matarsa bayan aurensu fiyeda yadda yasota a layi ya nuna mata kauna ya jata ajiki ya sanar da ita abinda yafi faranta masa rai ya bata Abinci a baki ya tarairayeta kamar jaririya cikin so da kauna... Shine mai kishin matarsa. Domin Sayyidil waraa Sallallahu alaihi wasallam yace: "duk wanda baya kishin matarsa bazai shiga aljannah ba". Shine wanda ya dauki aure amatsayin Ibadah, ba wai abin wasa ba ko kuma abin jin dadin rayuwa kawai ba.... Shine wanda ya dauki matarsa amatsayin abokiyarsa, kanwarsa, almajirarsa, kuma abokiyar shawararsa. Shine wanda ba ya zagin matarsa, baya cin mutuncinta, ba ya cin zalinta, baya ha'intarta koda a bayan idontane...... Shine wanda yake zaune da iyalinsa cikin amana da gaskiya da kyautatawa ba cuta ba cutarwa. Shine wanda idan ya fahimci halayen matarsa, yake hakurin zama da ita tare da kyautatawa domin neman rahamar Allah Ta'ala. Shine wanda idan zai yi magana da matarsa, zai fadi gaskiya babu yaudara ko karya acikin ayyukansa da zancensa. Shine wanda ya dauka a zuciyarsa cewar: Iyayen matarsa, Iyayensa ne. 'Yan uwanta ma 'yan uwansa ne. Danginta ma danginsa ne. Shine wanda yake daukar cewa farincikin matarsa shine farincikinsa. Kuma Problem dinta, shima nasa ne... Shine yake kokarin kiyaye sirrin matarsa, kuma yake kokarin Kare mata mutuncinta koda awajen 'yan uwansa ne, tare da hikima da.fahimtarwa. Shine wanda baya fifita matarsa akan 'yan uwansa, kuma baya tauye mata darajarta. Yana ba ma kowanne gefe nasa hakkinsa kamar yadda shariah ta tanadar Shine wanda ya tanadi ruwan afuwa da hakuri acikin zuciyarsa domin ya rika kashe wutar tashin hankali da bacin rai aduk lokacin da hakan ta faru tsakaninsa da matarsa. Shine wanda a kullum yake kokarin tarbiyyantar da iyalinsa akan rayuwar addinin Islama ba rayuwa irinta yahudu da nasaraba Shine wanda yake zaune da matarsa komai da'di komai wuya ba zai dena nuna mata soyayya ba wai don tafara yankwanewa ko kuma karfinta yafara raguwa. Shine wanda yake bawa matarsa compliments a duk lokacin datayi kwalliya ko kuma tayi girki komai rashin dadinshi. Miji nagari baya raki,baya ihu don yaji abinci yayi yaji ko gishiri yayi waya. Sai dai yace: "uwargida abincinnan yayi dadi iyaka, sai dai gishiri yayi mana shisshigi aciki".... Shine Wanda yakeda tausayi a duk lokacin damatarsa bata da lfy to shima bashida lfyr yana tausaya mata matuka yakan dauketa da kanshi ya kaita asibiti domin tausaya mata... Kunji kadan daga cikin halayen maza nagari.... Allah Yasa mazaje su gane, su sauke hakkinsu na kulawa da iyali, su daina ha'intar matansu, su daina yin dare a layi, ko kuma cin abinci a rumfar me shayi... Ya Allah ka bamu maza nagari... Su kuma ka basu mata nagari ameen... 

Yadda zaki mallake zuciyar mijinki!

1. Ki riqa yi masa halin mata, wato irinsu kisisina, shagwaba dss, don namiji baya son mai halin maza ta zama matarsa.
2. Ki zamo mai iya kwalliya. Idan kin kasance mai zaman gida ce to kici ado ko da kuwa baza ki fita ko zuwa ko ina ba.
3. Kada ki fara lissafowa mijinki matsalolinki ko na gida a lokacin da ya shigo, ki barshi ya huta tukuna ya samu nutsuwa.
4. Ki zamo mai kirki, ladabi da biyayya ga Mahaifiyar mijinki kamar yadda zaki so shima ya zamo kamar haka ga mahaifiyarki.
5. Ki dinga qarawa mijinki qarfin gwiwa akan abinda kika ga alamar yana nema ya karaya, hakan zai sa ya gwarzo a cikin maza.
6. Ki dinga fadawa mijinki cewa kina sonshi sau dayawa, dayawa dayawa, Aisha ?????? ???? tace Annabin tsira SAW ya kasance yana tambayarta qarfin soyayyarta gareshi, sai tace mishi kamar ‘zarge’ (wato dauri ko kulli wanta bazai kwance ba), sai ya sake tambayarta ‘yaya zargen yake’? Kuma ya kasance yana cewa da ita Allah ya saka miki da alkhairi Aisha, ina farin ciki da jin dadi dake fiye da yadda kike farin ciki dani!
7. Ki dinga yawan sada zumunci ga mutanen gidansu (kamar ziyartarsu, kiransu a waya dss).
8. Ki dinga bashi wani dan qaramin aiki a gida; kuma idan yayi aikin sai ki gode masa. Hakan zai sa ya qara dagewa.
9. Ki dinga qarfafa masa zuciya wajen yin aikin alheri
10. Idan yana cikin damuwa ki dan bashi lokaci, da yardar Allah sai kiga ya dawo dai dai.
11. Ki dinga yi masa godiya akan sama miki abinci da muhalli da yake yi, abune mai girma!
12. Ki tuna cewa mijinki ma yana da damuwa da farin ciki, saboda haka ki dinga tunawa dashi wajen yanke hukunci.
13. Idan mijinki ya nuna damuwa akan dan qaramin abu da kika yi masa to sai ki bashi haquri kuma ki dena.
14. Kiyi dukkan abubuwan da aka lissafo saboda Allah, sai kiga Allah ya sa miki albarka a cikin duk abinda kike yi.
Allah ya kawo mana albarka da yalwar arziqi da ta ‘ya’ya a cikin Rayuwar Aure!

Contact Form

Name

Email *

Message *

Translate

LATEST POST