ads:::

HANYOYIN KASUWANCI GUDA BIYAR A YANAR GIZO DA YA DACE KAYI

HANYOYIN KASUWANCI GUDA BIYAR A YANAR GIZO DA YA DACE KAYI A wannan babi nawa zan bayyana muku kasuwanci mabambanta guda biyar na yanar gizo da ya kamata duk wani mai amfani da yanar gizo ya fara domin cigaban rayuwarsa. 1. Sayar da Kayyakin da ake iya gani: Mafi shaharar kasuwancin yanar gizo shi ne sayar da kayyarkin da za a iya turawa abokin kasuwanci. Misali; idan kai mai aikin gadaje ne ko mai sayar da shadda ko atamfa ne kai tsaye zaka iya daukar hoton sana’arka ka saka a shafinka na yanar gizo tare da bayani kan ko wane daga cikin hotonan da kuma kudadensu. Daga nan za a sami masaya kuma zasu saya ka tura musu kai tsaye kuma hakan ya farune ta hanyar website dinka, hasali ma za a iya biyanka kai tsaye daga shafinka na yanar gizo zuwa asusun ajiyarka na banki. Don haka abu mafi sauki shine ka shirya shafin (Shopping ko eCommerce) daga nan sai ka sanya duk wani abin sayarwa da kake da shi a yanar gizo daga nan duk lokacin da mutane suka shiga a shafin naka na yanar gizo, zasu iya biyan kudi su saya kai tsaye. Bayan ka yi karbi kudin, sai ka aika musu kayan nasu wadanda suka saya. 2. Sayar da kayayyaki daga na’ura (Digital Product): abin nufi a nan shine, za a iya shirya littafai (e-books) ko hoto mai motsi (video), sautin murya (audio) ko kuma wani kumshi (software). Wadannan kayyakin sune kayan da suka fi sauki wajen sayarwa a shafukan yanar gizo da kuma saurin sayarwa. Irin wadannan kayyakin itan abokin hulda ya saya akan tura masa mashigar da zai shiga domin ya sauke kayan nasa da ya saya (link). Don haka ba a da bukatar hadasu wuri daya ko a dauke su zuwa wani wuri ko wata kasa ta mota ko jirgi zuwa ga abokin huldar kasuwanci. Amfanin irin wannan kasuwancin na zamani shine baka da bukatar tsara wasu kayyaki da kake tunanin ana da bukatar sai an gansu ido da ido sannan a aikasu zuwa ga masu su. Kuma wannan kasuwancin yana da sauki wajen kashe kudi idan muka hadashi da wancan da muka yi maganarsa a baya. 3. Yin aiki a shafukan yanar gizo: akwai shafukan yanar gizo da yawa da za a iya aiki kamar fiverr.com inda zaka iya ganin mutane masu yawan gaske da suka kware sosai wajen gudanar da ayyoka irin daban-daban wa jama’a kuma a mafi karancin kudi. Misali; a aiki daya zasu iya karbar N2150 idan kuma a kwatanta da dalar amirika 5USD. Idan har zaka iya yin aiki kamar zanen gidaje, tamfarin (logo), zane-zane, rubuce-rubuce, (online marketing) shirya hoto mai motsi (video animation) ko kuma (programming). To, zaka iya yi tare shahararrun mutanen da ke cikin wannan shafi ko makamancinsa a yanar gizo. Misali zaka iya shiga Freelancer sannan ka rubuta ire-iren ayyukanka. 4. Sayarwa wasu kayyayyakin su ko ayyukansu: Wannan shine abu mafi sauki kafar yanar gizo ko kuma kasuwanci da yafi ko wane sauki a yanar gizo. Anan kenan mai makun sayar da naka kayyayyakin ko ayyukan sai ka sayarwa wasu mutanen da nasu. Wannan shine mukafi sani da suna (Affiliate Marketing). Wane irin aiki ne wannan, idan ni affiliate ne kenan ba sai na shirya wani abu nawa na sayarwa ba, ba ni da bukatar tsara wasu kayyarki don jama’a?. kawai abin da ake bukatar da kai shine, ka kasance a kafar yanar gizo sai ka nemi kayyayyakin wasu Ko ayyukan wasu mutane, sannan ka nemi ka zama Affiliate don daukaka Sana’arsu da kuma ayyukansu, riki wannan a matsayin misali; idan ka shiga Amazon, zaka ga amazon (offer program) sun rubuta Amazon Associates. Idan ka shiga a wannan Associate program, zaka samu naka mashiga (link) na Amazon. To, daga nan sai kayi ta yadawa a wasu kafafen haka kuma zaka iya aikawa abokai da yan uwa da wannan mashiga (link) daga nan zaka dinga samun naka kaso na kinikin da suke samu daga wajenka. Idan an fahimta haka abin yake aiki, abu mafi kyau a cikin wannan shine, haka kawai ba kada bukatar sai ka mallaki naka shafin ko wasu kayan sayarwa ko ayyukan da zaka yiwa wasu mutanen, abin da kake bukata shine, ka yi rajista da (Affiliate program) idan har kana da ra’ayin yin hakan. Sannan kuma ka tabbatar affiliate program din ya kunshi kayan sayarwa masu yawan gaske. 5. Sayarda Filin Talta: Idan kana da shafin yanar gizo da ya shahara, duniya ta sanshi ko kuma kana da wani shahararren shafin yada labarai a kafar yanar gizo, to zaka iya sayarda filin talla a cikin sa domin samarwa abokan huldarka jama’a ko masaya sana’arsu ko kuma masu kananan kasuwanci domin taimaka musu su karfafa sana’arsu ko ayyukansu. Haka abin yake, idan kai sabo yafi kake dashi ko yafin yada labarai to dole ne ka dau hakuri zuwa lokaci mai tsawo har zai ka tabbatar ka samu karbuwa ga duniya sannan ka gabatar da ire-iren wadannan ababen.

Post a Comment

0 Comments

Contact Form

Name

Email *

Message *

Translate

LATEST POST