wannan tutorial din zamuyi bayanin yadda ake bude BLOG daga kamfanin google, wanda akafisaninta da blogger. Kuma zamuyi bayanin menene BLOG, kuma da amfaninshi.
Menene BLOG?
BLOG yana nufin wani shafi, ko wani guri, komuce wani ajine da mutane musamman masana harkar gina shafin yanar gizo, suke budewa, domin suna rubuta makalu(Articles), ko mujallu(Magazines), ko labaru(News update). Haka nanma wasu masana kamar malaman kwalejoji, da jami'o'i wato Lakcarori(Lecturers), suke budewa, domin suna koyarda wasu darrusa, na musamman, hade da hoto ko bidiyo, da sautin murya. Ganin cewa yanzu duniya, mafi yawanci wasu harkoki sunkoma kacokan ta internet, yasa mutane, ko kamfanoni dakuma wasu kungiyoyi, ko jam'iyun siyasa, suke bude BLOG, domin tallata hajarsu, ko watsala labarai, kokuma tallata manufofinsu ga jama'a mabiya wannan shafin nasu.
Amfanin BLOG?
BLOG yanada amfanoni dadama, amma bari mukawo koda guda biyar ne daga cikinsu, wanda mutane sukafi azahiri.
Sune Kamar Haka
Labarai
Iimi
Kasuwanci
Siyasa
Entertainment
Bari mudanyi bayaninsu, daya bayan daya, koda atakaicene, yanda mutane zasuyi saurin fahinta da ganewa.
LABARAI
Mafi yawan kafafen watsa labarai, suna amfani da BLOG, domin suna rubuta labaransu, ta yanda jama'a masu sauraronsu, zasuna kai ziyara domin sukaranta wa'annan labarai, harma suna iya ajiye ra'ayinsu, gameda wannan labarin da suka karanta.
ILIMI
Masana, ko muce malamai, masana ilimi suma sukan bude BLOG, domin suna rubuta bayanai, kokuma sakamakon bincike binciken dasukayi. Banda wannan ma, masana sukan bude BLOG domin suna koyar da dalibansu, musamman masu amfani da yanar gizo, darussa dadama.
KASUWANCI
Mafi yawa daga cikin kamfanoni, ayanzu sukanyi amfanida BLOG dan tallata hajarsu, ga jama'a har sukan iya siyar da wasu daga cikin abubuwan dasukeyi tacikinsa. Bayan haka sukanyi amfani da shafin BLOG nasu, domin sutallata guraben ayyuka ga masu bukata, idan suna dasu ta cikin wannan shafin nasu.
SIYASA
A wannan zamani idan muka lura, yan siyasa sun koma amfani da internet domin tallata manufofinsu ga jama'a. Sannan ta hanyar BLOG, masoya wannan dantakarar, kokuma wannan jam'iya. Kuma suna iya turawa wa'ancan yan siyasan ra'ayoyinsu, kuma nan take zasu ga wannan sakon yatafi ga wa'anda suka turawa.
ENTERTAINMENT
Mawaka, da yan wasan kwaikwayo sukan bude BLOG domin kara kusancinsu da masoyansu, kuma sukan tallata sabbin fina finansu, dakuma wakokinsu ta wannan hanyar, sannan mabiya wannan shafin nasu, anan sukan samu damar dakko sabbin hotuna na wannan dan wasa ko mawakin daya bude wannan BLOG din.
Kai! Nima ta hanyar BLOG nake bada gudunmuwata ga jama'a masusan koyan yanda ake abubuwa dadama awaya kokuma a interent.
Abubuwan Da'ake Bukata
Email na Gmail.
Kasaukar da template anan.
Kasaukar da FireFox.
Ko kasaukar da Chrome.
Ga Yanda Akeyi
Dafarko, kabude browserka, ammafa saida wa'anda muka lissafo asama. Kana budewa, saikarubuta www.blogger.com agurin rubuta url address, dake can sama, sannan saika danna GO, kokuma OK. Saika danjira kadan takama, idan takama zakaga takaika wani shafi, wanda zakaga background nashi yana canja kala-kala. To saika danyi kasa kadan, kawai kadanna kan inda aka rubuta CREATE YOUR BLOG, domin bude sabon blogger kenan.
Yauwa, kanayin yanda mukace kayi, zakaga takaika, inda zaka bude sabon blog naka, na blogger, mallakin google. To kaduba, zakaga gurin saka title, da address, dakuma gurin theme. Sai kashiga gurin Title, karubuta suna, ko taken blog din naka misali, take ko sunan nawa shine Fasaha, to kaima haka zakayi. Saikuma gurin saka Address, shikuma nan shine inda zakasa sunan dakakeso yazama shine url address naka, misali wannan shafin sunanshi https://arewapress1.blogspot.com/ to amma anan, kawai sunan zakasa, misali ninasaka fasaha24, to suda kansu zasu karamaka, yazama kamar haka https://arewapress1.blogspot.com/. Saikuma kazabi Theme, shikuma Themeshine wanda yake canja tsari, ko launi da kuma yanda ake ganin cikin blog, to kawai saikayi tick akan Themedinda kakeso kayi aiki dashi, idan kagama komai, kawai kayi kasa kadanna inda aka rubuta Create Blogkawai.
Toshikenan, yanzu mun gama bude sabon BLOG, na blogger, abunda yarage shine, muje mugwada posting acikin sabon blog namu. Bayan kagama bude blogger, zakaga takawoka cikin Dashboard na bloggerka, wato inda ake yin komai na bloggerka. To idan zakayi posting sai kaduba cikin Dashboard din, zakaga Posts to kadannashi zakaga yabudo maka wasu rubutu daga kasan Posts din, kaduba daga tsakiya, gamasu aiki da computer zakuga New Post, masu aiki dawaya kuma daga gefen dama zakuga New Post, saiku dannashi.
Daga nan, zai bude muku wajen yin sabon post, kawai saikasa Title na post din, saikuma kayi kasa cikin wannan katuwar box din, kasa post content wato bayanan cikin post din gaba daya, saikayi bangaren hannun dama, daga sama zakaga Publish, saika dannashi, kanayin haka shikenan kagama yin sabon post.
Yauwa, mungama komai cikin ikon Allah, munbude sabon BLOG, sannan kuma lokacin damuke budewa munzaba masa theme, daga baya kuma mukayi sabon post, to haka ake bude BLOGGER, kuma babu wata wahala, yanada sauki, sannan kuma bayacin lokaci domin zaka iya gama koma acikin minti, ko kasada haka.
A tutorial nagaba idan Allah yasa muna raye, zamuyi cikakken bayanin yanda akeyin sabon post a BLOGGER, tareda taimako wani application. Shima bashida wahala kawai kabi abu daki daki.
Anan ne mukazo karshen wannan tutorial din. Kuma wannan tutorial din, yaso yayi kamada wanda mukatabayi, abaya amma wancan tutorial din yanzu mun gogeshi. Bayan haka kuma, kuna iya temaka mana, a duk inda kukaga munyi wani kuskure, kokuma mukayi wani abunda kukega bahaka yakeba, zaku iya magana gyara, domin kowane dan Adam maiyin kuskurene, kuma idan mutum yayi kuskure yanadakyau asamu masu gyara masa. Bayan wannan kuma zaku iya turomana naku tutorial din, domin mukaru daku wasuma sukaru, yanda dukkanmu zamu karu baki daya.
Sannan karkuma manta, ako da yaushe muna farin ciki da ganin comment naku. Kuma kuna iya ajiye mana comment naku, a wajen comment da aka kebe akarkashin kowane darasi, dakuma tutorial a wannan shafin. Sannan muna bukatar kutemaka kutura wannan tutorial din zuwa ga wasu domin suma sukaru, zaku iya turashi zuwaga 'yan uwa, da abokan arziki, kodata dandalin sada zumunta na Whatsapp, Twitter, Facebook, Instagram, Email ne dasauransu. Mungode, sai mun hadu a darasi nagaba, kuhuta lafiya, sai anjima.
4 Comments
fallout anthology crack
the sims 4 snowy escape crack
Need for Speed Payback Crack