
KYAUTAR BUDURCI PART 1
Ra'uf,Rabi'u, da
Ridwan Yan uwan juna ne,uwar su daya ubansu
,ra'uf ne babba ,sai rabi'u sai ridwan ,yan asalin
jihar misau ne ,sunyi karatun boko da arabi,amma
ra'uf da rabi'u sun fi yin xurfi a boko,yayin da
ridwan ya maida hankali a gonarsu ta gado
,domin yana gama secondary yayi aure ,ya shachi
bangare a gdansu ya xaune da matarsa hauwa
,bayan shekara uku da aurensu su ka haifi
'ANWAR' , a lokacin rabi'u yayi aure da matars
ramla ,bayan ya samu aiki a NNPC ,shima ya tare
birnin abuja ,shekara biyu da auransu suka haifi
'ANAS', Rau'f baban boko shi medicine ya
karanta ,shine dai auren nasa daga baya baya ,
bayan kuma shine babba,ya kamalla karatunsa ya
samu zama consultant a asibitin AKTH ,ya
tamfatsa gdansa a darmanawa ya tare da
matarsa yar asalin kuwait' girman kano amma
mai suna 'lubna'........zuwa yanxu anwar na da
kanne uku adam,basma da bahijja ,yayin da anas
yake da kanwa guda daya aisha .......ra'uf,rabi'u
,ridwan dukkansu suna yin zumunchi mai tsafta
......... Duk da kowa garin da yake daman , ra'uf
da lubna sai da suka shekara biyar da aure
ALLAH ya azurta su ya mace ,ranar suna aka sa
mata suna 'zARINA' ........daga kanta lubna bata
qara haihuwa ba,duk wani so da gata sai suka
dorawa tilon yar su zarina............BAYAN
SHEKARA 16...
PART 2
'ANWAR RIDWAN' ,saurayi
kyakkyawa na ajin farko,miskili,nagartacce,dan
gaye ,mai tsafta ,dan kimanin 23 ,ya gama poly
dinsa .....yanxu haka ya samu admission BUK sun
bashi lvl 2 ,course din business admin .....yau
yake shirin barin misau izuwa kano ,xai xauna a
gdan yayan mahaifinsa Alh.Ra'uf,domin shine ya
sama mai admission ......... 'ANAS RABIU' .....dan
hutu ,dan gata ,mutanen abuja .....saurayi mai ji
da class da charisma ,dan kimanin 20......ana
kasar 'holland' ana hada deegree......... 'ZARINA
RA'UF' shalelen iyayenta,kyakkyawar gaske
,wanda kyanta ya samo asali gun mahaifiyarta
domin tama dara haj.lubna a kyau ,ga gashi ,ga
iya kwalliya ,duk gatan ta hakan bai sa ta
sangarche ba ,tana tarbiya dai dai
gwargwado,yanxu haka tana kan kuriciyarta wato
'sweet 16' ,amma in ka ganta sai ka rantse she's
18 saboda garin jiki,tana ss3 yanxu haka........
Anwar ya iso kano lfy ,ya doshi gdan 'aljannar
duniyar ' uncle dinsa Alh.ra'uf ,tarba iya tarba ya
samu ,domin hajiya lubna ,macece mai son
jama'a ,bayan an kaishi dakinsa ya natsa ,domin
lokacin da yazo zarina na skool , yana kwance
kan gado yana hutawa ........a wannan lokacin
zarina ta dawo tana part dinta abunta ,.domin
yanayin garin akwai hadari,ruwan sama at any
time,....ruwan sama akayi sosai ,zarina mayyar
ruwa ,ta faki idon mahaifanta ta nufi garaji ta
fara wanka da ga shimi sai 3qtr a jikinta ,tana
wanka tana tsalle, hakan yayi dai dai da anwar ya
zo yarufe windon dakinsa domin ruwan dake
shigowa ,tsayawa chak yayi tare da rintse
idanunsa yayi ,domin wani kibiya da ya soki
xuciyarsa ,hakan ya haifar mai da wani shock .
Dalilin hango beautiful Zarina dancing in the rain
...........a takaice dai Anwar an kamu ..
: KYAUTAR BUDURCI
: KYAUTAR BUDURCI
PART 3
Anwar cikin ikon Allah
ya fara zuwa makaranta,bayan an mallaka masa
mota (driver ya koya masa)tsakaninsa da zarina
gaisuwa ......suna jin dadin zama dashi,ba ruwan
shi da tsabgar kowa ,wato baida zaqewa ,yana
kama kansa sosai.........a yau alh.ra'uf ya
damqawa anwar amanar sauke zarina a skul
kafin ya wuche tasa makarantar ,hakan ya janyo
shakuwa mai tsanani a tsakaninsu ,amma
miskilanchin anwar bai sa zarina ta harbo jirgin
son da yake mata ba,ya bar wa xuciyarsa ,ita
kanta zarina ta yaba da anwar ,sai ta xauna tayi
ta tunaninsa,in basu hadu ba ,tayi ta kewarsa
,hakan na nuni da ce wa ta kamu amma ita kanta
ba ta sani ba .....ranaku ,satittika ,watanni sun
shude .......shekara ta bada baya ....zarina an
kamalla secondary ......anwar an lvl 3 ,zuwa
yanxu duk su biyun sunyi tsamo tsamo cikin
tafkin tekun soyayyar junansu ......amma sun
boyewa junansu ........sun damu da junansu
matuqa ,komai tare ,irinsu chin abinci ,fita
shopping ,qarin karatun qur'ani da litattafan
addinni......da sauransu ......ra'uf da lubna sun
dau haka a matsayin haduwar jini ,zallar kauna
da yan uwan taka ................ A yau Zarina ta
cika shekara 18 , ta zama cikakkiyar BUDURWA
,komai ya ji........ Hijabs sune abund zarina take
sakawa ,bisa umarnin yayanta kuma masoyinta
anwar ...... Anwar yana lvl 4 ynxu wato final year
,zarina kuwa an fara zuwa CAS ....... Yau Anwar
ya shirya leqawa misau kamar yadda ya saba duk
karshen wata ....alh.ra'uf ya hada mai tsarabar
da zai kai wa ridwan wato kanninsa....... ..zarina
hankalinta a tashe duk tayi narai narai da idanu
....anwar ya dubeta ya ce sweetsis kwana 10
kawai xanyi in dawo ,ga waya ,ga whatsapp we
will kip in touch, ta dubeshi da fuskar shagwaba,
amma yaya kasan zanyi missing dinka sosai,gdan
xai yi min fadi wit out u .....da kyar anwar ya
lallasheta yayi tafiyarsa .....suna masu kewa da
begen juna ............ ANAS ne tsaye a filin airport
din nnamdi azikwe dake abuja ,an dawo daga
holland tare da kwalin degree .....
[: KYAUTAR BUDURCI
PART 4
Iyayensa da 'kanwarsa
aisha,suka tarbeshi,suka wuce gida cike da
murnar dawowarsa,bayan kwana uku,alh.rabiu ya
cewa anas ya shirya zasu tafi kano gaba
d'ayansu daga kano su wuce misau,domin sada
zumunci.. Yau tunsafe ake shiryen shiryen isowar
alh.rabiu da iyalansa,karfe 5pm suka iso ,sai
murna ake,anas kuwa idanunsa na kan zarina
,domin ta mugun tafiya da imaninsa,karfe takwas
bayan sun kimtsa,ana kan dinning ana cin
dinner,zarina tana kitchen tana had'a citrus
salad,anas ya dubi dad dinsa,yace ni fa naga
mata a gidannan,alh.rabiu yace ga ka ga babanka
,saika gaya mashi,alh.ra'uf ya d'ago yace menene
d'ana,anas yana sosa kai yace zarina nagani
kuma nake so,alh.ra'uf ya murmusa yace da kai
da ita duk daya a guna,anas na baka zarina,ko
bayan raina ina mai bada wasiccin aurenku kai
da zarina,hakan yayi dai da sulalewar glass bowl
daga hannun zarina,mai dauke da citrus salad
....tirkashi
PART 5
Tashin hankalin da
zarina ta shiga bazai kwatantu ,a take ta tattaro
nutsuwarta ta juya ta bar gun .......... Tun daga
ranar ta kauracewa kowa a gidan ,ta kulle kanta
a daki ,in banda kuka ,bbu abinda takeyi,sallah
ma da kyar take rarrafawa tayi,ta rufe duka
wayoyinta ,in kaga tafito abinda xa ta kai bakin
salati taje nema a kitchen..... Anas kuwa murna
yake abun sa ,ya samu abunda rai ke
so,matsalarshi daya ,rashin ganin zarina ko da a
dining ne ,ita kanta aishar ba haduwa suke da
zarina ba balle yasa ran chusa kansa ko ta
bangaren kanwarsa ne...a nashi ganin wai kunya
ce ta hanata fitowa ,take gudunsa....... Alh.ra'uf
da rabiu shagalin gabansu kawai suke ,domin
Alh.ra'uf ya bugawa mal.ridwan waya cewan
yana buqatar yazo kano tare da iyalensa .....ana
san ran yau zasu ma zo...... Haj.lubna ta dubi
zarina 'lafiarki kalau kuwa ,kin hana kanki
walwala ,ba kya fitowa , ki kunshe kanki a daki,in
ma lamarin auren nan ne yasa kika maida kanki
haka,toh gwara ki cire damuwa a ranki ki rungumi
aurennan ,domin ko datsewar numfashinki ba zai
sa hana aurennan ba ,ko gawarki ne sai a wanke
an kai ,ke in banda abinki banga kina kula wani
ba,domin ko kare ban taba ganin yaxo gunki ba
.....ko kina da wanda kikayi wa
alkawarine ? ....shirun da zarina tayi ya bata
daman cigaba da magana da sigar lallashi ta dubi
zarina' kiyi hakuri ,ki zama mai juriya da
rungumar kaddara,ki yi biyayya ,zarina kiyi
biyayya ki rabu damu lafiya kinji........... Ta dubi
kofar da umman ta fice ,sai kawai ta fashe da
wani kuka mai ciwo, anwar kai nake so,kaine
farin cikina .akan ka nafara sanin so ,akanka
nasan dadin zama da masoyi ,akanka nasan
menene unconditional love,anwar meyasa baka
fadawa abbanka kana sona ba,meyasa baka furta
min so ,meyasa baka nunawa duniya kana sona
........toh sakarya shi ce miki yayi ya na
sonki,daga yace zai furtamiki muhimmiyar kalma
,sai ki dauka sonki yake ,haba zarina ki tsai da
hankalinki ,ki nutsu ....zuciyarta ta
nussasheta........shigowar su aisha,basma da
bahijja ya dawo ita daga tunanin da ta fada
......ta dubesu ......hakan na nuni anwar da yan
gidansu sun iso kenan ........nima na bisu da
kallo domin b3 na yayi low...
: KYAUTAR BUDURCI
PART 6
Zarina ta kokarta
ta saki jikinta ,ta fito ta gaisa dasu kawo
ridwan,aka hallara a dining karan cokali kawai
ake ji,anwar sai neman idon zarina yake ,amma
ita tasha mur 'domin ita haushinsa takeji ,anas
kuwa bakinsa uwa gonar auduga,sai fara'a yake
........... Bayan sallar isha kowa ya hallara falo
(familyn so cute) .... Alh.ra'uf yayi gyaran murya
...yace abunda yasa muka taru anan gaba dayan
mu shine,nariga na yanke hukuncin za'a daura
auran ANAS da ZARINA ,ANWAR da AISHA
...ranar juma'ar nan domin abu ne tuwo na mai
na ,aisha xata zauna anan ,zarina zata bi angonta
Abuja, Anwar saboda miskilanci baza ka iya gane
a wani hali yake ba , Anas kuwa sai hamdala
yake a zuci , aisha kuwa ko a jikinta ,domin
anwar ba mijin yadawa bane ,zarina kuwa sharce
hawaye tayi wayance ta duban anwar (anata
ganin kamar bai damu ba) ...... Alh.ra'uf ya ce
akwai mai magana ? ,kowa yayi tsit....haj.lubna
ta muskuta tace Alhaji anya ba'a yi gaggawa ba
,i da ka bari anyi shiri sosai ,ya dubeta yace 'ni
fa na gama magana ,ina damar in aurar da yayan
,kuma bahijja da basma na baku wata daya ku
fito naku mazajen , kowa na iya tafiya ,...... Iyaye
mata suka nufi dakin haj.lubna domin fara
tattaunawa akan shirye shiryen biki ...... Iyaye
maza kuwa restroom din Alh.ra'uf domin hirar
zumunci ,bahijja da basma suma suka wuce dakin
da aka sauke su , anwar ,anas ,aisha da zarina
kadai aka bari a falon , anas charaf ya tashi ya
matso kusa da sahibar tasa ,ko kallo bai isheta
ba ,ta tashi ,anwar ya miqe ya bi hanyar da
zarina ta bi ........a hanyar kitchen suka hadu
..........ya ja hannunta ,suka fice suka nufi garden
,suna xuwa ,kawai sai ya rungumeta tare da sakin
wani irin kuka mai ciwo 'zarina i cn xpress hw
mch ur love means 2me ' bansan taya na fara
sonki ,sonki abune da ya shigeni ba tare da
nasani ,ina sonki ,i love u zarina ......ta janye
jikinta ....ta juya mai baya ,tace anwar dole mu
rungumi kaddara ,its too late 2cry ,biyayya kam
ya zama dole ,soyayyarmu bata qare mu da
komai ba ,saima ta shin hankali, anwar ina sonka
,gangar jikina za'a kaiwa anas amma zuciyata
taka ce,ina sonka,akan ka nasan menene so ,
akan na fara sanin dadin so ,kuma akanka nasan
zafin rabuwa da masoyi ,....zarina kin yarda mun
rabu kenan ......ta dubeshi tayi murmushi mai
ciwo.......idan so cuta ne ,.....hakuri magani
ne......taja baya ta bar gun a guje ,tana mai
zubda hawaye............duk abunda ya faru
tsakaninsu yanxu , akan kunnen da idanun
........ANAS yafaru....
: KYAUTAR BUDURCI
PART 7
Yau alhamis wato jajiberin
daurin auren ANAS da ZARINA ,ANWAR da
AISHA,, hankulan masoya biyu wato anwar da
zarina ya kai matuqar tashi ,bbu walwala a
tattare dasu , komai ciki karfin hali suke yi , hatta
gyaran jiki da kunshi karfin hali kawai zarina
tayi..............har dare yayi ,yau bata ga anwar ba
,hankalinta ya tashi ,ga wani matsanancin son da
take ji yana taho mata har wuya ........yanxu
haka ta kwance ta kurawa cieling ido .....yanxu
gobe i war haka ,naxama matar aure,matar anas
.mrs anas , ....ta fashe da wani irin kuka ....ji
take kamar dama ta mutu ta huta ....... Anwar ba
da kai zanyi rayuwa ba,ba kaine uban yayana
ba,kaddara ta zaba min anas a matsayin mijin
aurena ........ta dubi agogo karfe 12:30 na dare ,
ta sauko daga kan gado ,ta nufi kofar fita dakinta
ta fito.....gdan tsit alamun kowa ya kwanta
......kawai sai ta nufi side din da anwar yake ,ta
nufi dakinsa ,ta murda kofar ta ji ta a bude ta
shiga ..........Ido biyo ta tarar da anwar ,idanunshi
a kumbure ,wato shima yana cikin halin datake
......ya dubeta a razane , 'lafia ki ka zo min daki
a tsohon darennan ' ta dubeshi .yaya anwar nazo
muyi ,sallama ,nazo muyi bankwana g.obe xa'a
zargamin igiyar auren anas......ya rintse ido ,yana
mai jin yaji yaji a zuciyarsa.......... Shiru ya
ziyarci gurin ....ta qarasa gabansa ta rusuna a
gabanshi tana mai cewa 'yaya anwar naxo ne in
yi maka KYAUTAR so , nazo in baka KYAUTA kafin
mu rabu ,nazo inyi maka KYAUTA a wannan dare
kafin a daura aurena gobe ,ba abunda mace take
tutiya ta kai gdan miji kamar BUDURCINTA ,
BUDURCI shine abunda ko wanne ango zai so ya
samu a gun amaryarsa, Yaya anwar ,BUDURCINA
naka ne kai kadai ,baxan iya sallamawa ko wani
namiji BUDURCINA ba ,kaine Namiji tilo da
yakamata Ka mallaki BUDURCINA . kamar yadda
zuciyata ta zama taka .......haka nakeson
BUDURCINA ya zama naka ......yaya anwar na
baka 'KYAUTAR BUDURCINA ...........(shin ana
haka kuwa?)....
: KYAUTAR BUDURCI
: KYAUTAR BUDURCI
PART 8
Anwar ya dubeta a
firgice ,ya miqar da it tsaye ,yana girgizata 'zarina
lafiarki kalau kuwa ,in mafarki kike ,ki farka, haba
wacce irin KYAUTA ne wannan , zarina u dnt hv 2
do dis ,kafin in san cewa u love me deeply ba ,i
wannan rashin tawakkali ne ,da rashin yadda da
kaddara ,zarina plz kiyi hakuri mu bar maganar
KYAUTAR nan ....... Zarina ta dubeshi da jajayen
ido 'anwar ashe baka sona .ashe son da kake be
kai so ba ,if u truly love me u better accept my
GIFT 2 u , ...... Anwar ya dubeta 'in har aikata
zina ,shine zai tabbatar miki da cewa ina sonki
,toh zarina naji na yadda bana sonki din ...... Ya
juya mata baya ....... Anwar ka gwammace
waninka ya rigaka kusantata ,ka yadda cewa
anas shi yafi chanchanta da ya mallaki
BUDURCINA ....... indai akan sonka ne ,anwar
bana gani bana ji ..........da akan in mallakawa
anas BUDURCINA gwara na rasa raina ....... A
firgice anwar ya juyo 'zarina nafison karban
BUDURCINKI cikin mutunci, a karka shin inuwar
aure ..... Ta dubeshi tace 'kuma kaddara ta hana
hakan ' saita fara cire kayanta .......har ya zamto
daga ita sai fatar jikinta ........anwar ya rintse ido
,wani abu na mai yawo a jiki , tana hawaye tazo
ta rungumeshi , kam kam ya riqeta , ya kaita kan
gado.........cikin halin kuka da bege ,da zazzafar
so .a wannan dare Anwar ya raba zarina da
BUDURCINTA .......
PART 9
3:00am ...suka
dawo hankalinsu ....zarina in banda kuka ba
abunda take ,ga zafin first tym ,ga kuma tarin
nadama duk da dai tasan masoyinta ta bawa
kanta ,ba ta da asara ... Anwar ji yayi kamar an
zare mah son zarina daga zuciyarshi .....fit!
Soyayyar zarina 8a fita daga zuciyarshi........ Ya
tashi ko kallonta baiyi ba ya fada toilet .......ita
haka taja kafa ta fice ta nufi dakinta ...toilet ta
nufa ta kimtsa kanta ......amma duk da haka
tafiyar tata sai a hankali ......... Ranar juma'a da
safe kowa ya hallara a dinning ...ana breakfast
.......zarina da anwar sun kasa hada ido ,ita
matsanancin kunyarsa take ,shi kuma haushi ,da
kiyayyarta ne fal xuciyarsa ,ba ta da wani daraja
a idanunsa,ta sashi ya aikata zina under d same
roof dt he's livn wit his parent .......bayan an
kamalla ,anas ya dubi iyayensa duka ukun wato
Alh.ra'uf ,rabiu da ridwan .....ya rusunna yace
yana da magana ......... Anas ya juye musu komai
dangane da soyayyar zarina da anwar ,yace a
gaskiya ban cancanti in auri zarina ba ,anwar ne
ya kamata ya aureta ,sun dade suna son juna
fada ne kawai basuyi ba ,amma abba ina neman
alfarmar da a bawa anwar zarina ,nikuma ko
bahijja da basma ne a zaba min daya daga
cikinsu .......Alh.ra'uf ya numfasa yace 'daman
kai kaganta kace kanaso ,tunda ka bar wa anwar
,da kai da shi duk dayane , sai a maida auren
kanshi..........wani sanyin dadi ne ya ziyarchi
zuciyar zarina tana mai hamdala ga rabbis
samawati Budar bakin anwar sai cewa yayi
,tsakanina da zarina bbu wata soyayya hasashe
ne dai irin na anas ........amma ni zabin aishar da
kuka zaba min shine zabina abba .......don bazan
boye muku ba aysha tafi zarina kwanta
mini.......kuma abinda yayi zarina shiyayi
aiisha......zarina ta kwalalo ido ......hmm wannan
shine ta leqo ta koma (kunga laifinsa? Ni dai
nace #GAME_OVER )
: KYAUTAR BUDURCI
PART 10
alh.ra'uf ya sauke
numfashi 'shikenan duk babu matsala,anas
daman kai kace kanason zarina,tunda yanxu ka
janye,toh anjima za'a daura auranka da
basma,bahijja da zarina kuma Allah ya kawo
muku mazaje,gaba dayanku duk daya kuke a
guna,bbu tilastawa' ,a haka aka gama cin abinci
aka watse da niyyar bayan sallar juma'a a daura
aurensu anwar,zarina jiki a sanyaye taja
kafafunta ta shige daki,ta rufo kofar ,idanunta
suka fara zubar hawaye,tana mai danasanin
abinda ta aikata a daren jiya,oh ynzu haka anwar
zai mini,oh Allah ina mai kunyar daga hannayena
in ro'keka gafara bisa abinda na aikata dalilin son
zuciya da rashin tawakkali,Allah na tuba ka
yafemin ,ka kawo min d'auki ga wannan halin da
na jefa kaina a ciki,a daidai lokacin haj.lubna ta
shigo,ta nemi gu kusa da zarina ta zauna ,a
sanyaye tace 'yanayinki kad'ai ya nunawa cewa
kamar an miki fyad'e zarina','dama fyad'e aka
min da da sauki wlh' ,zarina take fad'i a
zuciyarta,idanunta na zubda hawaye ,ta
labartawa haj.lubna komai dangane da daren
jiya,hannu akan kirji tare da kwalalo
idanuwa,haj.lubna ta maimaita kalmar 'KYAUTAR
BUDURCI' a firgice.
PART 11
hannu biyu haj.lubna
tasa tana jibgar zarina cikin 'kunar rai,tana had'a
kanta da katako gado,tare da zabga mata zafafan
mari,zarina ko motsawa batayi ba,sai da
haj.lubna ta gaji dan kanta ta kyaleta,tana cewa
'tir zarina,tir wlh,BUDURCIN dungurgum kika
d'auka ki ka bawa saurayi kyauta,wai ke gaki 'yar
dadi soyayya ko,wlh kin tabka kuskure
babba,kuma ni banga laifinsa ba,yayi min
daidai,toh mezaiyi dake bayan hakan ta faru,mace
anyi auran ,ta kai budurcinta gidan miji ,ya ta
'kare da wulakancin d'a namiji,ina ga toh ka d'au
budurcin ka bashi kyauta,sai kuma abinda hali
yayi,da yake Allah ba azzalumin bawansa
bane,anas bashi da hakkinki ,hakan yasa aurenki
dashi ya warware cikin sauki,ya kuma musanya
masa da wata,da kinyi hakuri ,da yau kin zama
matar anwar ,da kinyi tawakkali kin miqa
lamuranki ga Allah, da yau kin ga sakayyar mai
cike da khairan,amma ina! Sai kikayi gaban kanki
,ki ka dau budurcin kacokam kika bashi
kyauta,toh ynzu wa gari ya waya,baki da tsuntsu
,ba ki da tarko,kin rasa anwar,kin rasa anas,kin
rasa budurci,asara uku kenan,shi kuwa gashi can
za'a d'aura auransa ya kuma amsar wani
budurcin,bayan wanda aka bashi kyauta,zarina
kinyi kuskure mai mugun muni',zarina kuka take
kawai mai cin rai, tana mai dana sani wanda
hausawa sukace 'keyace,haj.lubna ta fice ta barta
anan..[kunga laifin haj.lubna?]
: KYAUTAR BUDURCI
PART END
karshe'
Bayan shekara 1
anas shi da matarsa basma sun wuce asia domin
a can yake aiki anwar da aisha suna zamansu lfy
,ya kamalla bautar kasa,yana aiki a kano.. Zarina
ta dawo so silent,ta mugun yin sanyi,cAs ta daina
xuwa,ta rungumi zaman gda da zaman daki,ibada
da istigifari kawai take,ta zamto abar tausayi ,har
haj.lubna da kanta ta sauko daga fushin da tayi
da ita,alh.rauf ya tmby lfy,amma kawai sunce
masa yanayin rayuwane ya maida zarina
haka,shima ya xuba mata ido.. Wata rana anwar
yaje misau,mahaifinsa mal.ridwan ya dubeshi
yace 'ina umartarka da kaje ka nemi auran
zarina,ko da baka sonta,ita tana sonka,domin
naga hakan idanunta ,kawaici kawai tayi a ranar
da anas ya fasa aurenta kai kuma ka nuna baka
ra'ayinta ',anwar bai da za6i illa ya bi umarnin
mahaifinsa,aka d'aura auren anwar da zarina ,ta
tare ,tsakaninta da aisha bbu matsala,amma a
idon anwar aisha ta fita daraja,saboda ya samu
budurcinta a karkashin inuwar aure ,sa6anin
zarina data bashi KYAUTAR BUDURCINTA ,ita
kanta zarina tasan KYAUTAR BUDURCI bai kareta
da komai ba ,domin a dalilin KYAUTAR BUDURCI
ta rasa SO,MUTUNCI,DARAJA,KIMA,a gun anwar
,ita kuma aisha a dalilin ta kai BuDURCINTA
dakin mijin aurenta ta samu SO,DARAJA,MUTUN
CI,KIMA, a gun anwar...sai dai muce Allah ya
bawa zarina da anwar zaman lafiya(tammat) ***
a nan nakawo karshen gajeren labarin KYAUTAR
BUDURCI ,gareku mata dan ALLAH ku kiyaye
budurcinku,domin budurcinku shine
martabarku,duk wuya duk rintsi,duk wulakacin d'a
namiji ,zaifi ki kai masa budurcinki bayan ya biya
sadakinki kuma an shaida an shafa fatiha,amma
KYAUTAR BUDURCI babba asara ce ga d'iya
mace ko da kuwa hakan na nufin faranta ran
wanda aka bawa Kyautar naku har abada
(c)Abdul'aziz Ililie Isma'il
: KYAUTAR BUDURCI
AREWAPRESS1.com.ng