Guguwar Tsunami Ta Kashe Mutane 43 A Indonesia
3 hours ago
Mahuakaciyar guguwar Tsunami da ta kada a gabar tekun Sunda Strait na kasar Indonesia da yammacin jiya Asabar, ta kashe mutane 43 kana ta jikata kusan mutane 600, a cewar hukumar kai agajin gaggawa ta kasar.
WASHINGTON DC —
Mai magana da yawun hukumar kai agajin gaggawa lokacin bala’i ta kasa ya fada a cikin wata sanarwa cewa an samu asarar rayukan ne a yankuna uku a kudancin babban birnin kasar Jakarta.
Hukumar tace daruruwar gidaje sun lalace da wasu gidajen otal-otal guda tara da kananan jiragen ruwa goma ne suka lalace.
Ma’aikatar hasashen yanayi ta kasar tace za a samu tashin guguwa a tsibirin Krakatoa mai fama da aman wuta da misalin karfe tara na dare a jiya Asabar, jim kadan bayan lokaci kalilan sai Tsunami ta tashi a daidai karfe tara da rabi na dare.
Wata sanarwa tace ana sa ran adadin mutane suka mutu zai karu saboda jami’ai basu iya kaiwa ga duk wuraren da mahaukaciyar guguwar ta shafa ba. Wata babbar hanyar dake hada yankin Serang da Pandeglang ta lalace.
A ranar 28 ga watan Satumban wannan shekarar ma girgizar kasa da mahaukaciyar guguwar Tsunami sun abkwa yankin tsibirin Sulawesi dake kusa da birnin Palu kuma sun kashe mutane sama da dubu biyu da 500 kana wasu dubu saba’in suka rasa matsunguanasu.
0 Comments